25 Janairu 2018 - 15:39
Masu Azabtar Da 'Yan Ci-Rani Sun Shiga Hannu A Libiya

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya nakalto cewa a yau laraba ne aka kama 'yan wata kungiya wadanda suke kama da azabtar da 'yan ci-rani.

Kungiyar ta kunshi 'yan asalin kasar Libya biyar da kuma wani dan kasar waje. An kama su ne bayan da suka azabtar da wasu 'yan ci-rani su biyar da a halin yanzu suke kwance a asibitin garin Sirt.

A cikin kwanakin nan an nuna bidiyon wasu bakaken fata wadanda aka kona gadon bayansu da zummar karbar kudade daga danginsu.

Sayar da bakaken fata a matsayin bayi a cikin kasar ta Libya ya fito fili ne a karshen shekarar 2017 da ta shude, wanda ta jawo yin suka daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa